Jide Omokore ya mayar da N200m asusun gwamnati
– Wata majiya a hukumar EFCC ta bayyana cewa Jide Omokore ya mayar da kudi N200m asusun gwamnati
– Omokore da wasu guda 5 ne suka gurfana a gaban watan babban kotun tarayya akan almundahanan kudi $800m
Jide Omokore, shugaban kamfanin Atlantic Energy Drilling Concept Nigeria Limited kuma abokin tsohuwar ministan mai, Diezani Alison-Madueke, ya mayar da kudi N200m asusun gwamnati.
Jaridar Punch ta bada rahoton cewa wata majiya a hukumar hama almundahana da yima tattalin arzikin kasa zagon kasa,wato EFCC ce ta bayyana hakan.
Majiyar tace: “A binciken da muka gudanar, mun gano cewa kimanin asusu 8 na Omokore a Skye Bank. Yawanci asusun na kamfnoni ne. wasu na nan a Marina, Adeola Hopewell da kuma wasu wurare a legas.”
KU KARANTA:Jide Omokore ya mayar da N200m asusun gwamnati
“Mun samu mun kwato N200m . ya bayar da takardan kudi da sunan gwamnatin tarayya kuma ya biya kudin zuwaga asusun gwamnatin tarayya.”
Hukumar hama almundahana da yima tattalin arzikin kasa zagon kasa,wato EFCC ta damke shi ne a watan yun akan laifin cewa ya hada baki da tsohuwar ministan mai Aliso Madueke wajen sace dalolin kudi wata kasauwancin man fetur.
Omokore da wasu guda 5 ne suka gurfana a gaban watan babban kotun tarayya akan almundahanan kudi $800m.
The post Jide Omokore ya mayar da N200m asusun gwamnati appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.