Atiku ba zai kai labari ba –tsohon shugaban PDM
– Tsohon shugaban jam’iyyar PDM Bashir Yusuf ya soki lamirin Atiku Abubakar da cewa tsohon mataimakin shugaban kasa sya zama tamkar macijin da ba ya ramin kansa ne
– Ya kuma ce Atiku na amfani da shugabannin jam’iyyar don cimma wani burin na son zuciya don kuma amfanin kansa kadai
Tsohon shugaban jam’iyyar PDM Bashir Yusuf ya ce, tsohon mataimakin shugaban kasa kuma jigo a jam’iyyar APC Atiku Abubakar na kokarin kwace jam’iyyar PDM ta karkashin kasa domin cimma burinsa na son rai a shekarar 2019.
Bashir wanda shugabannin jam’iyyar suka kore shi a ranar Alhamis 24 ga watan Nuwamba, ya zargi Atiku da kitsa korarsa, yayin da shugabannin jam’iyyar kuma ke cewa, “sun kori Yusuf ne domin ceto jam’iyyar daga mutuwar tsaye da ta ke yi a matakin kasa.”
KU KARANTA KUMA: Ra’ayi: Arewa da sauran gyara –Sheikh Gummi
A hirarsa da manema labarai Bashir ya ce, Atikiu na amfani Shugabancin jam’iyyar ne don cimma wani muradi na kansa, a cewar kafar yada labarai ta Premium Times Bashir na cewa: “Hakika na san tsohon mataimakin shugaban kasan da hannu cikin abin da aka yi min. Domin yana son ya yi amfani da jam’iyyar ne a matsayin wukar baya domin tsayawa takara a shekarar 2019, idan a jam’iyyar APC ba ta tsayar da shi ba.”
Tsohon shugaban ya kuma ce, daga aljihunsa ya rika tafiyar da jam’iyyar PDM, kuma tuni hakan ya soma durkusar da shi, kuma abin da kawai Atikun ya kmata ya yi, shi ne ya tambaye shi, amma sai ya bi ta bayan gida da kulle-kulle, amma tun da ya bullo ta wannan hanyar su zuba su gani.
PDM ta samu rajista a matsayin jam’iyyar siyasa ce a ranar 15 ga watan Agustar shekarar 2013 da mambobin da yawancinsu ‘yan gani-kashenin Atiku ne.
Ku biyomu a Tuwita a @naijcomhausa
The post Atiku ba zai kai labari ba –tsohon shugaban PDM appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Nigerian newspapers 24/7.