Hotunan gidan Biliyoyin kudi na Kuku
– Hotunan gidan Biliyoyin kudi na mai taimaka ma tsohon shugaban kasa Jonathan
– Kuku ya nemi kotu ta hana EFCC bincikar shi
– Yana kasar waje neman lafiya
Tsohon mai ba toshon shugaban kasa shawara
Kingsley Kuku, tsohon mai taimaka ma tsohon shugaban Kasa Jontahan keda wani gidan Biliyoyin kudade a garin Akure, babban birnin jihar Ondo. Kuku a halin yanzu baya kasar nan amma da alamu sannu babu jimawa EFCC zata kama shi.
Kuku wanda shine mai tsara shirin alfarma da shugaban kasa yayi ma tsagerun Nija Delta ya nemi kotu data sanya a dakatar da binciken da ake yi mashi. Amma a ranar 17 ga watan Febrairu, alkali mai shari’a Okon Abang ya bayyana cewa EFCC tana da ikon ta bincike shi akan abubuwan da yayi lokacin mulkin shi.
Alkalin ya bayyana cewa idan kuku yaki zuwa, EFCC nada damar da zata kama shi. Ya bayyana cewa yin hakan kuma baya da wata alaka da siyasa. Sahara Reporters ne suka samo hotunan. Gasu a kasa.
The post Hotunan gidan Biliyoyin kudi na Kuku appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.