CBN zata takaita kudin da za’a iya fitar wa cikin Bankuna
Yan Najeriya zasu iya shiga wani hali nan gaba kadan sakamakon kayyade yawan kudin da za su iya cirewa daga asusun bankunan su wanda babban bankin kasar watau Central Bank of Nigeria (CBN) zai iya yi zuwa N10,000 kacal saboda raguwar yawan kudin da mutane ke kaiwa ajiya.
Babban Bankin Najeriya
A wani rahoto dai da jaridar Punch ta wallafa ya nuna cewar daga watan April na 2015 zuwa watan Aprilu na 2016 kudin da ake kaiwa ajiya a bankunan kasar nan ya ragu da kashi 5.6 % cikin dari wanda kuma yakai kudi N1.03triliyan. Haka zalika ma darajar kadarorin na bankunan sun ta ragu ita ma.
KU KARANTA: Naira ta dara Dala daraja a kasuwanni a yau
Rahoton dai ya kara da cewa babban bankin na Najeriya ya bayyana cewa bankunan kasar na fama da matsaloli tun daga hau-hawar farashi zuwa tabarbarewar tattalin arziki har zuwa faduwar darajar danyen mai da dai sauransu.
Wannan rashin kudin ajiyar da bankunan ke samu ya sanya har bankunan kasar sun kara sa ma ma’aikatansu yawan kudi da kuma kwastomomin da zasu jawo masu domin gudun rushewar su. Wani babban jami’in bankunan kuma da aka nemi jin ta bakin sa ya bayyana yin asusun bai daya watau Treasury Single Account (TSA) a matsayin ummul-habaisin matsalar.
A cewar jami’in, “tunda gwamnatin tarayya ta dauke kudin ta daga bankunan kasar aka fara shiga matsalar”.
The post CBN zata takaita kudin da za’a iya fitar wa cikin Bankuna appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers.