Rashin tsaro: kiristocin Arewa sun gargadi Buhari, da gwamnoni
-Kiristocin arewa, karkashin jagorancin Yakubu Pam, sun gargadi shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnoni a yankin da su dauki kwakwaran mataki don kawo karshen rashin hakurin addini
-Sun nuna bacin rai akan kisan wasu mutane a arewa akan zargin aikata sabo ga Annabi Mohammed
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari
Shugaban kiristocin arewa ya gargadi, Shugaba Muhammadu Buhari, tare da gwamnoni a yankin arewacin Najeriya, da su daina sakaci da al’amurran da ya shafi tsaro. Gargadin yazo ne daga shugabannin addinin dake cikin jihohi 19 nq arewa da kuma birnin tarayya, Abuja, a wani jawabi a ranar Lahadi, a cewar jaridar Vangard.
KU KARANTA: Ina so motoci suyi aiki da gas – Obasanjo
An keta doka, musamman bi da caka wuka ga wani Francis Emmanuel da wasu matasa musulmai sukayi a yankin Kakuri na jihar Kaduna, domin cin abinci a watan Ramadan, da kuma kisan wata mace, kan zargin aikata sabo a jihar Kano. Shugabannin kiristan sun yi kira ga gwamnatin akan dauki mataki a gurare dan kare Kiristoci da guraren bautar su, da kuma kawo karshen kisan rashin adalci ga Kiristoci a yankin.
Reverend Yakubu Pam, chiyaman na kungiyar Christian Association of Nigerian, a yankin ya yi kiran a Jos, jihar Plateau, ya ce basu yarda da cewa wata kungiyar mutane akan kare hakkin addininta zasu iya kashe wata mace ba, Mrs Bridget Agabahime, a jihar Kano da wani Kirista namiji, Chimaije Emmanuel akan cewa yayi sabo ga Annabi Mohammed.
Ya umurci gwamnonin arewa, da su fuskanci nauyi da ya rataya a wuyansu, a matsayin masu kula da harkan tsaro a jihohinsu, da kuma ba da ingantaccen tsaro akan rayuka da dukiyoyin Kiristoci a jihohin su.
The post Rashin tsaro: kiristocin Arewa sun gargadi Buhari, da gwamnoni appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers.