Buhari ya yaba ma sojojin Najeriya kan kokarin su
-Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar wa sojojin Najeriya goyon baya daga gwamnati da kuma godiya kan aikin hatsari da suke yi
-Shugaban kasa ya bukaci hukumomin tsaro da su ci gaba da yaki da masu tayar da kayar baya da ta’addanci
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dauki alkawari ga sojojin Najeriya cewa zai goya masu baya a yakinsu, kan matsalolin tsaro dake faruwa a fadin kasar, kamar yan kungiyar Boko Haram da kuma yan’bindiga.
Shugaban kasar yayi sanarwan ne ta hanyar ministan tsaro, Mansur Muhammad Dan-Ali, a gurin kaddamar da manufofin Nigerian Army Resource Centre a babban birnin tarayya Abuja.
Ya kuma yaba ma nasaran da sojojin sukeyi a yakin Boko Haram, amma ya bukaci da bunkasa yawan kai hari ga kungiyar yan’ta’addan, cewa harkan tsaro shine babban abunda gwamnatinsa take so ta inganta.
KU KARANTA KUMA: Sojoji sun kashe yan kungiyar Boko Haram
An karanta sanarwan Kaman haka: “ I na so na bayyanawa kasar cewa, daya daga cikin muhimman abubuwa da gwamnatin nan take so shine habbaka hukumar sojoji dan suyi ayyukan su. Zamu ci gaba da ba da goyon baya ga sojojin Najeriya don ganin sunyi aiki nagartacce kuma ta biyasu hakkinsu.”
Shugaban kasan ya bayyana fatan cewa gwamnatin yanzu tare da hadin gwiwar hukumomin tsaro zata tsare Najeriya.
The post Buhari ya yaba ma sojojin Najeriya kan kokarin su appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.