Kotu ta garkame tsohon gwamna a kurkukun Kuje
Hukumar hana cin hanci da rashawa ta kasar nan watau Economic and Financial Crimes Commission (EFCC) ta samu umarnin garkame tsohon gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri.
efcc
Babbar kotun tarayya dake Abuja ce dai ta bada umarnin na kulle shi har sai gobe Juma’a 1 ga watan Juli. Tsohon gwamnan dai ana tuhumar sa ne da laifin haddama da babakere da dukiyar jama’a. Babban mai shari’a Ahmed Mohammed ne dai ya zartar da hukuncin tare da bada umarnin bayan da tsohon gwamnan ya musanta dukkan zargin da akeyi masa har guda 5 yau Alhamis 30 ga wata.
Hukumar ta EFCC ta gurfanar da tsohon gwamnan gaban kotun tare da wani kamfanin gine-gine na Mayim Constructions and Properties Ltd. Jim kadan bayan da tsohon gwamnan ya musan ta duka zargin dake yi mashi ne dai sai kotun ta kuma saurari bukatar sa ta neman beli amma kuma sai hakan bata samu ba saboda dan jinkirin da aka samu har zuwa gobe juma’a.
Daga nan ne sai kotun ta bayar da umurnin da a cigaba da tsare shi har sai sadda aka gama sauraron bukatar tasa. Shi dai Umaru Fintiri ya taba zama gwamnan Adamawa a matsayi na rikon kwarya a cikin shekara ta 2014 bayan da majalisar jihar ta tsige gwamnan na lokacin Murtala Nyako.
The post Kotu ta garkame tsohon gwamna a kurkukun Kuje appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.