An fidda Enyimba daga gasar zakarun nahiyar Afirika
Kulob din Enyimba ya sha kashi a hannun kulob din Mamelodi Sundowns na South Africa da ci 2 – 1 wanda hakan ne ya fitar da ita daga gasar zakarun na Afrika.
Mai tsare ragar Eyimba
Kulob din na South Africa ya samu nasarar fara cefa kwallo a zango na farko na wasan ta hannun Leonardo Castro a cikin minti na 42. Daga bisani ne kuma Oluwadamilare Ojo na Enyimba ya zura tashi shima a cikin minti na 59.
Masu masaukin bakin na South Africa sun samu damar zura kwallon tasu ta hannun Arendse. Kulob din na Enyimna dai ya zuwa yanzu ya rasa wasanni biyu kenan a jere.
Mai karatu zai iya tunawa cewa a baya kulob din na Enyimba ya sha kashi a hannun kulob din Zamalek na kasar Egypt a garin Port Harcourt da ci 0 – 1.
The post An fidda Enyimba daga gasar zakarun nahiyar Afirika appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.