Da yiwuwan Dasuki zai kasance a tsare tsawon rayuwarshi
Kotun hukumar tattalin arziki ta kasashen Afrika ta yamma, wato Economic Community of West African States ko ECOWAS a takaice ta jingine yanke hukuncin a kan karar da tsohon mai bada shawara a kan harkokin tsaro kanar mai murabus Sambo Dasuki ya kawo mata inda yake kalubalantar tsaronsa da hukumar tsaro ta farin kaya ke masa ba bisa kan ka’ida ba tun cikin watan Disamba na shekarar da ta wuce.
Kanarl Sambo Dasuki (rtd)
Mai shari’a Friday Nwoke wanda ya saurari karar ranar 16 Mayu ya sa yau (Alhamis 20 Yuni, 2016) ta zama ranar yanke hukunci bayan ya saurari bayanan lawyoyin Wanda ake tuhuma Robert Emukperuo da na Gwamnatin tarayya watau Tinjani Gazali.
Lawyoyi, ‘yan jarida da masu bin kadin shari’ar sun je kotun ranar Laraba 29 Yuni, 2016 da tunanin za’a yanke hukunci amma sun yi mamakin da aka ce masu ba’a gama rubuta hukuncin shari’ar ba amma za’a fada ma lawyoyi sabuwar ranar da aka sanya.
Tsohon Mai bada shawarar yana mai bukatar kotun da tayi watsi da tsaron da ake masa, da kuma rike masa dokiyarshi, ta kuma hana gwamnatin tsareshi ba bisa ka’ida ba
KU KARANTA : Kotun zabe ta tabbatar da nasarar David Mark
A cikin karar, lauyan Dasuki Robert Emukpoeruo yana bukatar kotun da ta umurci a biya Dasuki N500 miliyan saboda tsare shi da akayi, shiga gidanshi da kwace masa dukiyarsa ba bisa ka’ida ba.
The post Da yiwuwan Dasuki zai kasance a tsare tsawon rayuwarshi appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.