Lauyan da ke karar shaidar satifekit din Buhari ya janye
Lauyan da ke karar rashin shaidar satifekit din Shugaba Buhari ya janye
– Lauyan da ke karar cewa Buhari bai da takardun zama Shugaban Kasa ya janye karar daga kotu
– Lauyan dai yayi ikirarin cewa Shugaba Buharin bai taba rubuta jarrabawar WASC ba
– Yace ana so a ga bayan sa
Lauya Nnamdi Nwokocha-Ahaaiwe, lauyan da ya shigar da karar Muhammadu Buhari cewa bai da satifeket din da ake bukata wajen tsayawa takarar Shugaban Kasa ya janye karar daga kotu. Jaridar THIS DAY ta rahoto cewa Nnamdi Nwokocha-Ahaaiwe ya nemi a janye shari’ar daga kotu a ranar 27 ga watan Yuni, sai dai ba a san dalilin da ya sa yayi hakan ba. Ana dai ana ta rade-radin cewa barazanar da ake yi ma rayuwar sa ta sa ya sa ayi watsi da karar. A baya lauya Nwokocha-Ahaaiwe ya koka kan cewa ana masa barazanar ya janye karar ko a hallaka sa. Ya fada ma ‘yan jarida a baya: “Hakika na damu, ba ma ni kadai ba; ‘yan uwa da abokan arziki ma haka. Ana mani barazana, sai dai ni ba sakarai bane. Saboda haka jama’a su san cewa muddin wani abu ya faru da ni, ko da sunan wani hadari…”
KU KARANTA: SHUGABA BUHARI YA JINJINA MA SOJOJIN NAJERIYA
Lauyan ya zargi ‘yan Najeriya da yin tsit game da harkar, yace duk masu karyar surutu sun yi shiru kamar ba su san abin da ke faruwa a Kasar ba. Kasar nan tayi rashin Cif Gani Fawahemi, Gwarzon namiji, inji lauyan. Shi dai lauyan da ke zaune a Jihar Legas yayi karar cewa Muhammadu Buhari ba sa da takardun da ake bukata wajen tsayawa takarar Shugaban Kasa yana musanta cewa Shugaban ya rubuta wata jarabawar shaidar kammala karatun sakandare (WASC) na Cambridge a shekarar 1961.
KU KARANTA: KOTU TA YANKE SHARI’AR KARAR TAKARDUN BUHARI
The post Lauyan da ke karar shaidar satifekit din Buhari ya janye appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.