Yan Neja Delta sun gargadi Buhari game da Maritime
Shugaban kungiyar matasan Neja Delta watau Niger Delta Youth Association Worldwide Victor James ya bayyana damuwa ganin yadda gwamnatin tarayya ke shirin soke ginin jami’ar Maritime dake Okrenkoko.
Buhari
Shugaban ya bayyana damuwar tasa ne cikin wata sanarwa da ya ba manema labarai ciki hadda NAIJ.com wadda Stanley O. Efe ya sanya ma hannu. Kungiyar tace soke ginin jami’ar zai kawo ma mulkin shugaba Buhari matsala babba.
Victo James har wa yau ya yi wannan gargadin ne a wani taron manema labarai da yayi a garin Ingila. Yace: “Bai kamata a tsaida ginin Jami’ar ta Maritime ba, kamata yayi a cigaba da yin ta don kuwa zata kawo cigaba sosai a yankin na Neja Delta. Sokewar babban rashin adalci ne da danniya da ake ci gaba da yi wa yankin duk kuwa da yadda gwamnatin tarayya ke cigaba da anfana da yankin.”
Mr. James ya cigaba da nuna rashin gamsuwar sa da yadda sojin Najeriya suka mamaye Gbaramatu inda kuma ya bukaci da sojin su ba ma zauna yankin hakuri.” Gwamnatin Najeriya dai ta tsaida cigaba da ginin jami’ar ta Maritime ta kuma bukaci da a maido duk kudin da aka fidda domin gina ta a baya.
The post Yan Neja Delta sun gargadi Buhari game da Maritime appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.