An janye tuhumar da akeyima Neymar
Rahotanni da dama sun ruwaito cewa an janye tuhumar da akeyi wa dan kwallon kungiyar Barcelona kuma dan kasar Brazil Neymar tare da mahaifin sa a kan cinikayyar sa.
Neymar Jr.
Mai shari’a Jose de la Mata na kotun kasar Spain din ne dai ya kori karar bayan da wadanda suka shigar da ita suka bukaci hakan. Shi dai Neymar din ana tuhumar sa da kin bayyana ainihin kudin da aka saye shi daga tsohon kulob din sa na Santos zuwa Barcelona.
Dukkanin wadan da ake tuhumar dai sun musanta zargin a gaban kotun da ta fara sauraron shari’ar a cikin watan Fabrairun wannan shekarar. Shi dai dan wasan ya kara rattaba hannu a kan yarjejeniya da kulob din na Barcelona wanda zai sa ya tsaya har sai 2021.
A wani labari mai kama da wannan dai kuma Messi da mahaifin sa an yanke masu hukun cin dauri har na watannin 21 a gidan fursuna a bisa samun su da laifin da akayi na kin biyan harajin da ya haura €4m.
The post An janye tuhumar da akeyima Neymar appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.