El-Kanemi sun samu nasara, Enyimba sun sha kashi
Ga dai yadda wasannin da aka buga jiya asabar a sati na 26 na ci gaba da gasar kungiyoyin kwallon kafar kasar nan.
Elkanemi Warriors 3-1 MFM FC
Su dai kulob din na El-kanemi sun cigaba ne da samun nasara a filin wasan su dake garin Maiduguri a jiya asabar bayan da suka lallasa kungiyar MFM FC na garin Legas da ci 3 – 1.
Samuel Mathias ne dai ya fara zura wa El-kanemi kwallon tun a cikin mintuna 10 na fara gasar. Hussain Bata kuma daga bisani ya kara a cikin minti na 36 sannan kuma sai Kinnedium Nelson ya zura ma MFM FC kwallon su a minti na 55. Daga baya kuma aka kara musu ta hannun Danniel Japhat a cikin minti na 65.
A can karin Owerri kuma Enyimba ce ta sha kashi a wannu Heartland da ci 1 mai ban haushi. Dan wasan bayan Enyimba ne Chinedu Udoji dai yayi laifi a cikin gidan gol wanda hakan yayi sanadiyyar alkalin wasa ya bayar da bugun fenarati.
Dright Ejike kuma na kulob din Heartland ya zura kwallon bayan da ya buga. A haka dai akyi ta buga wasan har aka tashi. Yanzu haka dai Enugu Rangers ne ke jagorantar teburin bayan da suka samu nasar a saman Abia Warriors ranar Juma’ar da ta gabata.
The post El-Kanemi sun samu nasara, Enyimba sun sha kashi appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.