Gwamnatin tarayya na shirin horar da yan boko haram 800
-Kimanin yan boko haram 800 da suka tuba gwamnatin Najeriya zata horar
-An jero sana’oi 12 daban daban da za’a horar da yan kungiyar a kai
tubabbun yan kungiyar boko haram
Gwamnatin tarayya ta bayyana a ranar Litinin 1 ga watan Yuli, cewa ta yi dukkan abunda ya kamata domin fara shirin horar da tubabun yan boko haram 800 cikin yankin arewa maso gabas. Birgedia-janar Bamidele Shaffa, mai kula da al’amuran tubabun yan kungiyar Boko Haram, ya fada wasu taron manema labarai a jihar Gombe cewa tubabun yan boko haram zasu zo jihar Gombe ba da jimawa ba don koyan horo, cewa an gama duk wani shiri da za’ayi domin fara aiki a sansanin.
A cewar Xinhua, tubabun mayakan zasu koyi wani horo a sansanin, wanda zai basu daman komawa garuruwansu daban daban. Shaffa yace kimanin hukumomin gwamnatin tarayya 14 harda hukumomin tsaro zasuyi aiki a sansanin.Yace za’a horar da tsofafin mayakan sana’oi 12 daga fanni daban daban. Shaffa yace daraktan daukar ma’aikata na kasa baki daya zai samar da duk wani abu da za’a bukata domin horon.
KU KARANTA KUMA: Wani mutumin kasar Sin ya kashe kansa a jihar Lagas
A halin yanzu, ma’aikatar gaggawa ta kasa tace ta ba sojojin Najeriya kayayyaki domin kai tubabun boko haram din jihar Gombe. Sani Sidi, Darakta-Janar na hukuma, ya tabbatar da bayar da kayayyakin a lokacin taron da akayi kira ga Gwamna Ibrahim Dankwambo na jihar Gombe. Yace kayayyakin sun hada da abinci da wadanda ba abinci ba domin taimakawa kokarin sojoji a gurin shirin na horar da mayakan boko haram a kasar. Yace jihar Gombe ta kasance ta farko da ta karba bakoncin wannan shiri bisa ga wuraren dake a kasa, ba kamar yanda aka tsara da farko ba, na fara shirin a jihar Jigawa.
The post Gwamnatin tarayya na shirin horar da yan boko haram 800 appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.