Shugaban kasar Togo yazo Lagos domin bunkasa kasuwanci
NAIJ.com ta ruwaito cewa shugaban kasar Togo Faure Gnassingbe ya sauka Lagos ranar 1, Agusta, 2016 domin ziyarar matatar mai da Dangote ya gina kan kudi $14 billion a unguwar Lekki ta jihar.
Faure Gnassinge (
Gnassingbe ya Iso filin jirgin sama na Murtala Muahmmed da karfe 8:10 na safe inda gwamna Akinwunmi Ambode tare da Aliko Dangote da manyan mukarraban gwamnatocin tarayya dana jiha suka tarbe shi. Ana zaton Ambode zai tattauna da shugaban Togon hanyoyin da kasar zata iya sa jarinta.
KU KARANTA : Tattakin marasa goyon bayan gwamnati ya kare
Ana sa ran matatar mai ta Dangote zata iya tace gangar danyen mai 650,000 kowace rana wanda zai sata zama mafi girma a duniya
The post Shugaban kasar Togo yazo Lagos domin bunkasa kasuwanci appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.