Gwamna Bello ya sallami SSG, ya maye gurbinsa nan take
-Gwamna Bello bai fadi dalilin korar tsohon SSG din ba
-Bello ya maye DanyYa da Alhaji Ibrahim Isa Ladan nan take
-Ladan har ya kama aiki
Gwamna Abubakar Sani Bello n jihar neja.
Gwamnan jihar Neja Abubakar Bello ya sallami sakataren gwamnatin jihar Alhaji Umar Danyaya daga aiki ranar 1, Agusta cewar rohoton The Punch inda tan take ya maye gurbinsa da Alhaji Ibrahim Isa Ladan, wani tsohon shugaban karamar hukumar Borgu
Yayin da yake gasganta rohoton, kwamishinan watsa labarai da al’adu Jonathan Vatsa yace “har an kaddamar da Sabon SSG”, ya ci gaba da cewa gwamnan ya gode ma tsohon SSG kan ayyukan da yayi ma jihar.
KU KARANTA : Manajan Banki ya kashe kansa kan bashin naira miliyan 350
Dama akwai korafe-korafe game da nadin Danyaya cikin 2015, yayin da mutane da yawa ke cewa sai a cire shi domin tabbatar da rabon mukamai ga bangarorin jihar guda ukku bisa ga adalci
The post Gwamna Bello ya sallami SSG, ya maye gurbinsa nan take appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.