Matasan PDP sun bukaci NJC ta tsige mai shari’a Okon Abang
– Wani gungun matasan jam’iyyar PDP da ake Kira (PDPNYF) ta bukaci hukumar shari’a ta kasa NJC da ta gaggauta tsige alkalin kuma ta caje shi da “rashin da’ar alkalci”
– PDPNYF ta roki tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, da ya sa baki cikin rikicin jam’iyyar adawar
Yayin da mai shari’a Okon Abang, ya zartar da hukuncin da ya kori kwamitin wucin gadi na PDP wanda sanata Ahmed Makarfi ke ma shugabanci, matasan ja’iyyar na kira da cire alkalin
Baya ga haramta kwamitin na Makarfi, mai shari’a Abang ya hana kwamitin gudanar da taron kasa na Jam’iyyar da aka shirya yi ranar 17, ga Agusta a garin Port Harcourt. Amma kwamitin na cewa sai sunyi taron.
KU KARANTA : Shugabannin PDP na jihohi sun mara ma Makarfi baya
A cewar mai gudanar da PDPNYF na kasa Usman Austin, a wata sanarwa da ya bayar yana cewa “bai kamata shari’a ta zama wurin boyon masu laifi ba, ta bayyana karara mai shari’a Okon Abang ya maida wurin shari’a ya zama wurin saida hukunci ga mai iya saye. Muna Kira ga jama’a da su tashi tsaye su nuna rashin amincewar su da halin rashin da’ar alkalci wanda mai shari’a Okon Abang ke nunawa. Wannan ba illa ne kawai ga damokradiyya ba, barazana ne ga ‘yancin dan adam da darajar bangaren shari’a”.
The post Matasan PDP sun bukaci NJC ta tsige mai shari’a Okon Abang appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.