Yan sanda a jihar Ribas sun koka game da yawan safarar makamai
Sabon kwamishinan yan sanda na jihar Ribas Francis Mobalaji Odesanya ya bayyana cewar yana shan matukar wahala a jihar duba da yadda ake samun rahotannin yawan safarar makamai.
Kwamishinan yan sandan ya bayyana hakan ne a dai-dai lokacin da sojojin kasar nan suke kaddamar da ruguje wasu gidaje da ake kyautata zaton maboyar barayi ne da kuma sauran yan ta’adda a unguwanni da kuma wasu titunan babban birnin jihar Port Harcourt.
Bayan samamen da sojojin suka kai sun samu nasarar cafke wadansu da ake zargin barayi ne har su 142. Jaridar Leadership ta ruwaito cewa shugaban yan sanda ma dai ya bayyana damuwar sa game da yadda ayyukan ta’addanci ke kara karuwa a jihar lokacin da wata tawagar hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar ta kai masa ziyara a ofishin sa.
Shugaban yan sandan haka ma ya sha alwashin daukar matakan da suka kamata don danin an shawo kan matsalar a jihar ta Ribas. A cewar sa: “Tabbasa yan sanda suna iya bakin kokarin su, suna yin kokari sosai wajen ganin anyi zabe cikin kwanciyar hankali a jihar.
“Babbar matsalar yan zu dai itace Jihar Ribas tayi kaurin suna wajen safarar munanan makaman.
A bangare guda kuma jami’in hulda da jama’a ta rundunar yan sandan jihar Captaun Eli Lazarus ya bayyana a wata hira da yayi da manema labarai cewar: A jefin safiyar ranar Lahadi ne 31 ga watan Yuli wasu sojoji daga rundunar sojoji ta 2 suka kaddamar da wani samame a kan titin Lagas, Abuja da wasu boyayyan wurare a garin Port Harcourt a ci gaba da akeyi da yaki da ta’addanci da rashin da’a a jihar Ribas.”
The post Yan sanda a jihar Ribas sun koka game da yawan safarar makamai appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.