Naira nanan yadda take a yau watau N381/$1 a kasuwa
Darajar takardar kudin Najeriya watau Naira na nan yadda take a yau talata 2 ga watan Agusta kamar dai a jiya litinin din.
Mai karatu zai iya tunawa cewa a baya dai cikin watan Janairu babban bankin kasar nan ya hana yin cinikayyar kudaden bajen a kasuwannin bayan fage saboda a cewar sa babu isassun kudaden a wancen lokaci. Daga baya kuma sai babban bankin ya fito da wani tsarin yin canjin na daban da nufin kawo sauyi a kasuwar canjin da kuma farfado da darajar ta Naira.
Ya zuwa yanzu dai hakan bata fara samuwa ba ganin yadda darajar kudin Naira din ta fadi har ya zuwa N375 a yanzu din.
The post Naira nanan yadda take a yau watau N381/$1 a kasuwa appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.