Ya mutum bayan hawa palwayan wuta a taron siyasa
Wani saurayi dan shekara 20 dan asalin kasar Brazil da ake tunanin mabaraci ne ya rasu ta hanyar wutar lantarki bayan hawa palwayan wutan lantarki.
dan saurayin ya rasu a yayin taron gangamin neman kuri’a da dakatacciyar shugaban kasar Brazil Dilma Rouseff tayi. Mamacin na sanye ne da kananan kaya, kuma ya kasance yana nishadantar da jama’a ne a yayin taron siyasan a yankin Aracaju na kasar Brazil.
Sai dai, an samu labarin cewa jama’an dake wurin sun gargade shi da ya sauka daga kan palwayan bayan ya makale akan palwayan, amma sai yaki ji, yaki sauka, kuma ya kara hawa saman palwayan kusa da inda manyan wayoyin wutan ke daure.
Dagan nan kawai sai ya fado bayan wuta ta ja shi, inda kafin ya fado zuciyarsa ta fashe, yana fadowa kuma ya fasa kai, a haka dai ya mutu kafin a isa zuwa asibiti. Allah ya kiyaye gaba, wasu mutane dai suna jin dadin wasa da rayukansu.
The post Ya mutum bayan hawa palwayan wuta a taron siyasa appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.