Dan wasan Arsenal Jack Wilshere ya samu rauni
Yanzu haka dai dan wasan Arsenal na tsakiya Jack Wilshere ba ya buga wasannin sada zumunci da kuma sharar fagen da kungiyar sa keyi sakamakon raunin da ya samu a kwanakin baya.
Rahotanni kuma sun nuna cewar zai yi jinyar sati 1 ne kamar dai yadda mai horar da kungiyar Arsen Wenger ya fada. Makaru dai zai iya tuna cewar kakar wasannin da ta gabata ne ma kawai dan wasan ya taba buga wasanni 30 shekara 8 bayan zuwan sa kungiyar. Dan wasan dai bai buga wasan da Arsenal din ta samu nasara ba akan Chivas na kasar Mexico da ci 3 – 1.
Mai horar da yan Arsenal din Arsene Wenger dai ya shaidawa manema labarai cewa: “Dan wasan watau Welshere yan fama ne da matsala a gwiwar sa. Ba wata babbar matsala bace don haka muna sa ran ya warware daga jinyar sa nan da mako 1.
Arsenal are know to be very involved with pre-season
Rahotanni dai sun nuna cewa dan wasan ya samu rauni wanda ya sa shi jinya har sau 11 tun daga 2011 wanda kuma ya sashi yayi jinyar kwanaki 390. A wani labarin kuma kungiyar ta Arsenal a ci gaba da wasannin da sukeyi na sada zumunci za su kara da kungiyar Man city a garin Gothenburg a ranar Lahadi mai zuwa.
The post Dan wasan Arsenal Jack Wilshere ya samu rauni appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.