Labarai da suka yi fice a yau Talata 2 ga watan Augusta
Manyan labarai da sukayi fice daga jaridun a yau Talata 2 ga watan Augusta.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, Jubrin ya bukaci hukumomin shari’a da su fara bincike da hukunta wasu shugabannin majalisa su kuma kaisu gidan wakafi saboda zargin yin sama da fadi a kan kudin kasafi na shekara 2016.
Ya fada haka ne a jiya, lokacin da yake zantawa da manema labarai a hedkwatan yan sanda dake babban birnin tarayya Abuja.ya kuma rubuta takarda kan kakakin majalisar Yakubu Dogara, mataimakin sa, Yussuf Lasun , Alhassan Doguwa, Leo Ogor da wasu yan majalisa 9.
A cewar jaridar The Guardian, dakarun sojoji sun kai dauki kauyen Kaima na karamar hukumar Kolokuma/Opokuma na jihar Bayelsa a jiya Litinin 1 ga watan Yuli, domin dakatar da shirin da’awar jumhuriyar Niger Delta da kungiyar Yan bindiga mai suna Adaka Boro Avengers (ABA) ke shirin yi.
KU KARANTA KUMA: Ma’aikatan NNPC 50 na da hannu cikin zamba na milliyan 15
Daga jaridar Daily Sun kuma, munji cewa, jami’an yan sandar yankin Festac sun ceto wasu jarirai 3 da aka yasar. An kama mahaifiyar daya daga cikin jariran a lokacin da take yunkurin ajiye jaririn sati uku da haihuwa, kusa da wani gidan mai a hanyar 21 Road.
Daga karshe, jaridar Vanguard ta ruwaito inda, gwamnatin tarayya ta nada sababbin jami’ai 17 a ma’aikatar ilimi.
The post Labarai da suka yi fice a yau Talata 2 ga watan Augusta appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.