EFCC ta bayyana dalilin damke Abu Sidiqu
–Hukumar hana Al mundahana da yima tattalin arzikin kasa zagon kasa watau EFCC ta bayyana dalilin da yasa ta kama manemi labara Abubakar Usman .
–An baiwa Mr. Usman beli kuma za’a sake shi idan ya cika shaidun da aka nemeshi da ita.
Kakakin hukumar EFCC, Wilson Uwujaren , yayi Magana akan dalilin kama Abubakar Usman abu sidiqu ,wani magoyi bayan shugaba Buhari. Jawabin tace : “Hukumar hana Al mundahana da yima tattalin arzikin kasa zagon kasa watau EFCC ta a yau kama Abubakar Usman Sidiq, wani mai shafin sada zumunta saboda laifin saba yanar gizo.”
An damke mai shafin Abusidiqu.com ne a gidansa da ke kubwa , Abuja a ranar litinin ,8 ga watan agusta kuma ana gudanar da tambayoyi akan laifin da ya saba dokan amfani da yanar gizo. An rigaya da an bashi beli kuma za’a sake shi idan ya bada shaidun.
KU KARANTA : Aragizon kasafin kudi : Jibrin ya cigaba da gashi
Kama Mr. Usman ta tayar da hankalin mutane a shafukan yada zumunta ,har an yi sabon shafin a sake abusidiq a shafin twita.
Idan aka kama shi da laif, Mr. Abubakar Usman zai zama mai shafin yanar gizo na uku da za’a kama bayan an kama Seun Oloketuyi da Emmanuel Ojo a 2015 karkashin dokan da tsohon shugaba jonathan ya sanya.
The post EFCC ta bayyana dalilin damke Abu Sidiqu appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.