Muna neman Ibrahim Shema ruwa a jallo – EFCC
Hukumar hana almundahana da yima tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC ta alants a neman tsohon gwamnan jihar katsina,Ibrahim Shema ruwa a jallo.
EFCC ta alanta neman shema
Hukumar hana rashawan ta ce tana neman shine ruwa a jallo saboda gunduguzu,tsawwala kwangila, kama karya,karkatar da kudin al’umma da babakeren biliyoyin kudi.
KU KARANTA: Patience Jonathan na rokon EFCC ta sakammata kudinta
Kana EFCC tace ta mika goron gayyata ga Shema lokuta bila adadin tun 1 ga watan Disamba amma bai amsa ba.
Dan shekara 59 wanda dan asalin karamar Hukumar Dutsinma ne a jihar Katsina,tsohon gwamnan jihar ne daga 2007-2015.
The post Muna neman Ibrahim Shema ruwa a jallo – EFCC appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.