Wani Ango yaba mutane mamaki, sakamakon rawar da yayi mai ‘kayatarwa a ranar aurensa
Yawancin mutane suna son suyi auren bazata, wanda mutane zasu dunga tunawa dasu, tare da murna samun haihuwar fari, suka yi kokarin shirya yin wani abu da zai burge mutanen da sukazo wajen. Saboda haka suna kashe lokaci mai tsawo suna tunanin abinda zasuyi domin su birge dandazon mutanen da suka gaiyata.
Sannan kuma akan ba ma’auratan fili domin su nishadantar da jama’a.
Anan wani ango ne yayi rawan ban mamaki a ranar auren sa. Wannan angon mai suna Jeff Wehrke ya yanke shawarar baiwa mutane mamaki ta hanyar yin rawar aure wacce zata kayatar da Jama’a, saboda haka shi da amaryasa sunyi abunda suka sanya mutane shuru da bakinsu.
Da farko dai angon kamar bai iya rawar ba, amman daga baya sai gashi sai gashi ya baiwa amaryar mamaki ita da kanta, sakamakon rawar da yayi. Amman daga bayan wani dan lokaci saita dawo wajen angon nata sukaci gaba da rawar nasu tare.
Wannan abun mamaki ne.
The post Wani Ango yaba mutane mamaki, sakamakon rawar da yayi mai ‘kayatarwa a ranar aurensa appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.