An kama wasu masu satar mutane a Calabar (Hotuna)
– Wasu da ake zargi masu satar mutane ne daga jihohin Delta da Enugu sun shiga hannu a garin Kalabar ta jihar Kross Ribas
– An kama wadanda ake zargi da wanda suka sace, suna kuma kokarin tserewa da su a inda matasa sujka cim musu suka kuma yi tsirsra tare da lalata motarsu
Rana ta kwacewa wasu da ake zargin masu satar mutane a garin Kalabar a yayin da suke kokarin sace wani.
A wani bayani da kuma hotuna da wani gidan Talbijin ya mai suna APC TV ya watsa a dandalin sada zumunta da muharawa na Facebook na cewa, wasu mazauna a garin Kalabar sun cafke wasu da ake zargin masu satar mutane ne sun sato wani.
An yi wa masu satar mutanen tsirara an kuma lalata motarsu a cewar rahoton, sai dai a yayin da wasu ke nuna rashin dacewar yi musu tsirarar, wasu kuma na ganin dacewar hakan a matsayin gargadi ga masu aikata irin wannan hali.
Wasu kuma na cewa, a wannan lokacin na karshen shekara, da kuma matsowar bukuwan Krisimeti da sabuwar Shekara, aikata miyagun laifuka na dada karuwa.
kalli wasu karin hotuna na wadanda ake zatgi da satara mutanen da kuma yadda jama’a su yi musu tsirara.
Shin hakan ko ya dace? Aiko da naka ra’ayin a shafinmu na Facebook ko kuma Tuwita a @naijcomhausa
The post An kama wasu masu satar mutane a Calabar (Hotuna) appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Nigerian newspapers 24/7.