Bam ya tashi a tashar mota a Borno
Wani Bam ya tashi a tashar mota Muna a da ke garin Maidugurin jihar Borno
Wani tashin Bam a Maidugurin jihar Barno
A cewar kafar yada labarai ta Sahara Reporters, Bam din ya tashi ne a wata tasha da ke cikin garin Maiduguri da ake kira tashar Muna.
Bam din ya tashi ne da misalin karfe 9 na daren Laraba 23 ga watan Nuwamba.
Babu da cikakkaken rahoton yadda abin da ya faru, da kuma bayanin rasa rayuka, ko wadanda suka jikkata a tashin bam din da ake kyuatata zaton ‘yan kungiyar Boko Haram ne suka ta da shi ba.
KU KARANTA KUMA: Rundunar sojin sama sun yi ma Boko Haram ruwan wuta
A wani labari kuma rundunar sojin Najeriya ta yi wata arangama da wasu mayakan Boko Haram a inda ta hallaka 7 da daga cikin ‘yan ta’addan
A wata sanarwa da Kakakin rundunar sojin Kanar Sani Usman Kuka sheka ya sa hannu ta ce, sojoji na ta Bataliya ta 119 a karkashin dibishin na 8 da ke kauyen Kangarwa ne suka fafata da a ‘yan ta’addan a inda sojin suka hallaka su, wasu kuma suka tsere da raunuka.
Sanarwar ta ce, an jikkata sojoji 5 an kuma kai su asibiti a inda suke karbar magani.
Haka nan kuma a ranar Talata wasu rahotanni na cewa, ’yan ta’addan sun kai wani hari kauyen Dasa a inda sojojin suka fatattake su.
The post Bam ya tashi a tashar mota a Borno appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Nigerian newspapers 24/7.