Buhari ya ciri tuta a taron shuwagabannin kasashen Afrika da Larabawa
Shugaban kasa Muhammadu Buhari halarci taron budewa, sa’annan ta halarci zaman tattaunawa na kwararru daya gudana a taron shuwagabannin kasashen Afirka da na Larabawa a Malabo kasar Equatorial Guinea.
Da fari dai shugaba Buhari ya samu tarba irin na karamci daga gwamnatin kasar Equatorial Guinea, sa’annan a yau ake sa ran shugaban zai dawo gida Najeriya daga bayan kammala taron daya bada muhimmanci kan habbaka dangantaka tsakanin kasashen Larabawa dana Afirka musamman a fannin daya shafi kasuwanci da cinikayya, hadi da inganta tattalin arzikin kasashen.
KU KARANTA: An tilasta ma barauniya cin kashinta bayan taci duka
Hadimin shugaba Buhari ta fannin kafafen watsa labarai Femi Adesina yace taron zai yi duba da matsayin da aka kai wajen aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma a baya yayin taron karo na 3 daya gudana a kasar Kuwait a 2013.
Sa’annan shugaba Buhari ya samu ganawa da wasu shuwagabannin kasashen larabawa don sake duba ga yarjejeniya daban daban da aka cimmawa tsakanin kasashen da Najeriya don inganta su, musamman wadanda suka shafi harkar noman da samar da ababen more rayuwa.
Zaku iya bin labaran mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa
The post Buhari ya ciri tuta a taron shuwagabannin kasashen Afrika da Larabawa appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Nigerian newspapers 24/7.