Добавить новость
World News in Dutch
Новости сегодня

Новости от TheMoneytizer

Zaben Ondo: Jimoh Ibrahim ya ragargaji Fani Kayode

– Dan takarar gwamna a daya bangaren jam’iyyar PDP a zaben jihar Ondo Jimoh Ibrahim, ya mayarwa da  Femi Fani Kayode martani bisa wasu kalamai ya yi game da takararsa

– Femi Fani Kayode ya zargi Jimoh Ibrahim da neman satar takarar gwamnan jam’iyyar PDP ta bayan gida

Femi Fani-Kayode bakinsa ba ya haila a harkar siyasa

Hamshakin attajiri Jimoh Ibrahim ya mayarwa da Femi Fani-Kayode martani dangane da wasu kalaman da yayi kan takarar da yake yi a matsayin gwamna a daya bangaren jam’iyyar PDP karkashin  Ali Modu Shariff.

Dan kasuwan da ya koma harkar a siyasa, a wasu sakwanni da saka a shafinsa na Tuwita, ya ce, yana mai alfaharin cewa shi attajiri ne da ya kai matsayin Biloniya, kuma ba a taba zargin mahaifinsa da cin amanar kasa ba, kuma bai taba auri-saki ba, ko kuwa mace sama da daya ba, kuma duk da tarin dukiyarsa bai taba zaman fursuna a gidan yari na Kuje ba.

A sakon na Tuwita Jimoh Ibrahim ya kuma kira Fani Kayode wanda ba shi da alkibla a rayuwa,“…mutumin da zai iya yi maka waka da kida da kuma rawar mokosa idan har za ka ba shi tuwo.”

A wani sakon kuma yana mai cewa, “idan ka ga wanda ya san Femi Fani-Kayode, ga sako zuwa gare gare shi, NI BILONIYA NE KUMA BA NA SHARI’A DA EFCC.”

Attajirin dan siyasa kuma mai lambar yabo na OFR, a wani sakon yana mai cewa ga Fani Kayoden, kafin shekara 2019 zan taimaka in samo kwararrun masana kimiyya na duniya da za su yi maka magani cutar da ke damunka a kwakwalwa.”

KU KARANTA KUMA: An sauke sunan Jimoh Ibrahim a matsayin dan takarar PDP

Tun farko dai, a wasu jerin sakwanni ta dandallin sada zumunta da muhawara a ranar Laraba 23 ga watan Nuwamba, Femi Fani-Kayode ya caccaki dan siyasan, a inda ya kira shi da ma handami, mai kokakarin kwace takarar gwamnan jihar Ondo a ta bayan gida.

Femi Fani Kayode tsohon Ministan sufurin jiragen sama ne a zamanin mulkin Obasanjo, kuma jigo ne a jam’iyyar PDP, ya kuma taka muhimmiyar rawa a babban zaben shekarar 2015 da jam’iyyar ta sha kaye.

Ku biyomu a Tuwita a @naijcomhausa

The post Zaben Ondo: Jimoh Ibrahim ya ragargaji Fani Kayode appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Nigerian newspapers 24/7.

Читайте на сайте


Smi24.net — ежеминутные новости с ежедневным архивом. Только у нас — все главные новости дня без политической цензуры. Абсолютно все точки зрения, трезвая аналитика, цивилизованные споры и обсуждения без взаимных обвинений и оскорблений. Помните, что не у всех точка зрения совпадает с Вашей. Уважайте мнение других, даже если Вы отстаиваете свой взгляд и свою позицию. Мы не навязываем Вам своё видение, мы даём Вам срез событий дня без цензуры и без купюр. Новости, какие они есть —онлайн с поминутным архивом по всем городам и регионам России, Украины, Белоруссии и Абхазии. Smi24.net — живые новости в живом эфире! Быстрый поиск от Smi24.net — это не только возможность первым узнать, но и преимущество сообщить срочные новости мгновенно на любом языке мира и быть услышанным тут же. В любую минуту Вы можете добавить свою новость - здесь.




Новости от наших партнёров в Вашем городе

Ria.city
Музыкальные новости
Новости России
Экология в России и мире
Спорт в России и мире
Moscow.media






Топ новостей на этот час

Rss.plus





СМИ24.net — правдивые новости, непрерывно 24/7 на русском языке с ежеминутным обновлением *