An canza dan takara ana daf da zabe
– Hukumar zabe watau INEC ta tabbatar da cewa ta bi umarnin kotun kasa
– Kotun daukaka kara tace lallai Jegede ne dan takara a zaben gwamnan jihar Ondo
– Kotu tace Eyitayo Jegede ne dan takara ba Jimoh Ibrahim ba, INEC tace ta yarda
Eyitayo Jegede
Kotun daukaka kara ta rushe hukuncin da Babban Kotun Tarayya ta yanke kwanakin baya. Kotun tace lallai Eyitayo Jegede ne dan takara na Jam’iyyar PDP ba Jimoh Ibrahim ba kamar yadda aka umurta.
Hukumar zabe ta Kasa watau INEC tace ta ji ta amince da cewa Eyitayo Jegede SAN ne wanda zai rike tutar PDP a zaben da za ayi 26 ga wannan wata. A da baya dai Alkali Abang na Kotun Tarayya ya bada Hukunci akasin haka inda y ace Jimoh Ibrahim ne dan takara.
KU KARANTA: Dole a dage zaben Jihar Ondo-Fayose
Hukumar zabe ta Kasa watau INEC tace tayi watsi da umarnin da karamar Kotun ta bada a watan baya, za kuma ta sauya sunan dan takara Jimoh Ibrahim da na Tayo Jegede kamar yadda doka tace.
Jiya ne dai Gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose ya nemi Hukumar zabe ta Kasa watau INEC da ta dage zaben na Jihar Ondo domin Jam’iyyar PDP ta shirya da kyau.
A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa
The post An canza dan takara ana daf da zabe appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Nigerian newspapers 24/7.