Osinbanjo ya yi ganawar sirri da gwamnoni
Mataimakin shugaban Najeriya ya yi wata ganawar sirri da manyan jami’an tsaron kasar da kuma wasu gwamnoni na yankin Naija Delta.
A cewar jaridar The Nation, ganawar ta sirri an yi ta ne a ofishin mataimakin shugaban kasar da ke wani bangare na babban dakin taro na fadar gwamnatin kasar. Gwamnonin da suka halarta sun hada da gwamnan Bayelsa, da na Rivers, da na Delta, da na Edo, da kuma na Abia.
KU KARANTA: Fayose ya yaba ma shugaban kasa Buhari
Karamin ministan mai na kasar Ibe Kacikwu da Usani Uguru da kuma minista mai kula da al’amura Naija Delta duk sun halarci ganawar a lokacin da ake aiko da wannan labari. Bayan da tsagerun Niger Delta Avengers suka ci gaba da ta da bama-bamai a inda ake hako man fetur, gwamnatin Najeriya ta sanar da cewa ta kafa wani kwamiti wanda zai tattauna da tsagerun.
A cewar Kachikwu, wanda ya sanar da shawarar da gwamnatin da yanke a safiyar yau, ya ce gwamnati ta yi yunkurin ne domin dakatar da yawan hare-haren da ake kai wa wuraren wanda hakan ya sa yawan man da ta ke hakowa ya fadi zuwa ganga miliyan 1 da 500,000 a kowacce rana. Ya kuma kara da cewa kwamitin zai yi aiki ne a karkashi kulawar ofishin mai ba shugaban kasa shawara ta hanyar tsaro.
The post Osinbanjo ya yi ganawar sirri da gwamnoni appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers.