Kungiyoyin Biafra sun yi bata kashi kan Avengers
-Kungiyar Biafra Independence Movement, (BIM) watau kungiyar neman ‘yancin Biafra ta nisanta kanta daga hadin kai da Niger Delta Avengers.
– BIM ta cigaba da cewa, hanyar lalama itace hanyar da zasu bi wajen neman ‘yancin kan kasar Biafra.
– Kungiyar ta gargadi daya daga cikin masu goyon bayan MASSOB Mai suna Madu cewa zata tona mashi asiri idan basu canza manfarsu ta Neman ‘yancin Biafra ba.
Al’amurran tsagerun Niger Delta Avengers NDA ta kawo rabuwar kawuna tsakanin ‘yan neman kasar Biafra a cikin kasar.
Yayin da wasu a cikin masu goyon bayan Biafra suna alakanta kansu da ‘yan MEND, wasu a cikinsu na nisanta kansu da kungiyar, suna masu cewa hanyar masalaha itace hanyar da zasu bi wajen neman ‘yancinsu. Rohoton Jaridar Vanguard na cewa a baya-bayan nan, kungiyar BIM ta nisanta kanta da maganar NDA. Hakan ya Faru daga jawabin da ta bayar ranar Talata 21, Yuni 2016.
Kungiyar matasa ta Movement for the Actualization of Sovereign State of Biafra (MASSOB),na cewa bata da wata alaka da NDA, haka kuma bangaren MASSOB na chief Ralph Uwazurike bashi da wata yarjejeniya da wata kungiyar tsageru.
KU KARANTA: Biyafara ba za ta yiwu ba – APC
Yayin da BIM ke maida martani game da jawabin goyon bayan NDA da wani bangaren MASSOB da shugabanta Mai suna Uchenna Madu yayi taci gaba da cewa hanyar zaman lafiya ita ce hanyar da zasu bi wajen neman ‘yancin Biafra. Kungiyar ta ci gaba da yima jama’a gargadi suna masu cewa, zasu tozarta duk wanda bai canza ra’ayinsa ba game da hanyar neman Biafra har da shi Madu.
A nashi maida martanin, shugaban MASSOB Uchenna Madu yayi watsi da gargadin da BIM ta bayar. Ya cigaba da cewa, daga ranar da aka dakatarda da Ralph Uwazurike daga shugabancin MSSOB ya kuma gaya ma duniya cewa BIM itace sabuwar kungiyar shi ta neman Biafra.
The post Kungiyoyin Biafra sun yi bata kashi kan Avengers appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers.