Zlatan Ibrahimovic zai kammala komawa Manchester United
Jaridar Daily Mail ta bayyana cewa shahararren dan kwallon nan dan kasar Sweden Zlatan Ibrahimovic zai kammala komawarsa zuwa kulob din Manchester United a gobe Juma’a. Anyi ta rade-raden cewa Ibrahimovic din zai koma Manchester ne dai tun bayan barin sa PSG. Rahotanni da dama kuma sun bayyana cewa dan kwallon ya yadda da kwantaragin […]
The post Zlatan Ibrahimovic zai kammala komawa Manchester United appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.
Jaridar Daily Mail ta bayyana cewa shahararren dan kwallon nan dan kasar Sweden Zlatan Ibrahimovic zai kammala komawarsa zuwa kulob din Manchester United a gobe Juma’a.
![Zlatan Ibrahimovic](https://i.onthe.io/vllkyt4bs0rh2c4il.e258e434.jpg)
Zlatan Ibrahimovic
Anyi ta rade-raden cewa Ibrahimovic din zai koma Manchester ne dai tun bayan barin sa PSG. Rahotanni da dama kuma sun bayyana cewa dan kwallon ya yadda da kwantaragin shekara 1 da kulob din. Rahotannin dai suna kuma cewa dan wasan yana dab da koma ne kulob din na Manchester don kuwa jira kawai akeyi kwantaragin sa ta kare da PSG din yanzu haka.
A wani labarin kuma mai sauraro zai iya tuna cewa Ibrahimovic din ya bada sanarwar ajiye wa kasar sa ta Sweden kwallo tun bayan kashin da kasar ta sha 1 – 0 a hannun Belgium. Dan wasan dai ya zura wa kasar tasa kwallaye 62 a cikin wasanni 116.
The post Zlatan Ibrahimovic zai kammala komawa Manchester United appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.