Sojojin Najeriya sunyi tattaki na 6.5
‘Yan Najeriya tare da Rundunar Sojin kasar da ma Kwamitin wasannin ‘Olympics’ na Kasar (NOC) sun yi murnar bikin ranar ‘Olympics’ ta duniyar wannan Shekara jiya, Asabar a Abuja. Ana wannan biki ne a ranar 2 ga watan Yuli. Sojojin Najeriya da ma sauran mutanen Kasar; maza da mata sun shafe tafiyar fiye da kilomita 6 a Garin Abuja.
Shugaban Sojojin Kasan Najeriya, Laftana-Janar Buratai ya jagoranci tawagar wannan tattakin ne daga tsohon filin fareti na Unguwar ‘Area 3’ zuwa ‘Area 10’ na cikin Garin Abuja, Birnin Tarayyar Najeriya. Janar Buratai yace Sojin Najeriya na cikin duk wata harka da ta shafi motsa jiki, yace duk abin da ya shafi motsa jiki, to Soji na son a dama da su. Janar Buratai ya kira ‘yan Najeriya da su zama masu motsa jini don su kara lafiya. Shugaban Sojojin Najeriya yake cewa: “Mutanen Kasa su kula da lafiyar su, su rika motsa jinin su a kodayaushe, hakan zai kara lafiya da tsawon kwana.” Sojojin Najeriya da ‘yan bangaren wasannin Kasar, har ma da sauran Jama’a maza da mata su ka halarci wannan tattaki da aka yi a Birnin Abuja.
KU KARANTA: RYAN GIGGS ZAI BAR MANCHESTER
Shugaban Kungiyar wasannin Najeriya (NOC) Habu Gumel yayi godiya ga duk wadanda suka hallarci wannan tattaki, haka nan ya mika takardar shaida ga Laftanar-Janar Buratai, shugaban Sojojin Najeriya da kuma Solomon Dalung, Ministan wasannin Kasar da kuma Alhaji Muhammadu Bello Musa, Ministan harkokin Birnin Tarayyar Abuja.
KU KARANTA: DAN WASA YA SHA ALWASHIN JEFA KWALLO.
The post Sojojin Najeriya sunyi tattaki na 6.5 appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.