Buhari yayi ma IGP,AGF gargadi – Alibaba
Alibaba ya tofa albarkacin bakinsa akan tsare mutumin da sanya ma karensa suna Buhari, yace shugaba buhari yayi gargadi da sifeto janar na yan sanda da kuma babban lauyan tarayya. Ya rubuta : “Shugaba Muhammadu Buhari dattijon arziki ne. Hakazalika kuma shugaban kasa msi ci ne . kada ayi komai domin bata sunansa ko gwamnatin […]
The post Buhari yayi ma IGP,AGF gargadi – Alibaba appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
Alibaba ya tofa albarkacin bakinsa akan tsare mutumin da sanya ma karensa suna Buhari, yace shugaba buhari yayi gargadi da sifeto janar na yan sanda da kuma babban lauyan tarayya.
Ya rubuta :
“Shugaba Muhammadu Buhari dattijon arziki ne. Hakazalika kuma shugaban kasa msi ci ne . kada ayi komai domin bata sunansa ko gwamnatin sa. Amma wadannan magoya bayanshi masu ca akan zancen karen nan, ku sairareni , wannan shine turban da Jonathan ya hau ya zama abin kunya.”
“Bazaku iya fada mini cewan kusan makonni da dama da aka fara zancen wanan mutumi da ya lakaba wa karensa suna buhari, mutanen da ke kusa da buhari ko ma’aikatan sa basu fada masa abinda ke faruwa ba. Shin wannan ne matsalan da ke damun kssar mu. Fulani makiyaya nawa ne suka kashe mutane aka gurfanar da su kaman yadda ake ms mutumin nan.”
KU KARANTA : Najeriya zata ci ribar karewar darajar naira na wata biyu da farawa
“Kawai da muna jin ihun mutane masu shiga sharo ba shanu da sunan soyayya ko biyayya. Bari in fadi wannan ,kuma ba zan sake magana a kai ba. Shugaban kasa yayi gargadi ga Sifeto janar na yan sanda da kuma babban lauyan kasa. Akwai al’amuran da suka fi muhimmanci akan zancen kare da ake ta zuwa kotu akai. Maras aikin yi.”
The post Buhari yayi ma IGP,AGF gargadi – Alibaba appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.