Kamfanin jirgin Arik air sun koma aiki
Gidan talabijin na tarayya NTA ta bada rahoton cewa kamfanin jirgin Arik air zata cigaba da aiki a ranan Laraba, 14 ga watan Satumba, bsyan ta kulle aiki sanadiyar bashi.
NTA ta lakwato NAN cewa wata jawabi a shafin yanar gizon babban kamfanin jirgin ya ce zasu cigaba da aiki misalin karfe 11 na safe saboda ta biya bashin.
Jawabin tace : “Arik air, kamfanin jirgi mafi girma a yammaci da tsakiyar afrika na sanar da cewa gobe laraba, 14 ga watan satumba, misalin karfe 11 na safe zamu cigaba da aiki. Muna baiwa Jama’a da kuma kwastamominmu shawara suyi watsi da duk labari da suka ji na cewa kamfanin ta kasa biyan kudin man jirgi da kuma cewa kamfanin inshoran da Arik ta ke sun cire hannunsu daga al’amarin ta.
KU KARANTA:Dan Najeriya mai safarar kwayoyi ya shiga hannu
“Duk da cewan anyi karancin man jirgi kuma ya shafi jiragen sama a kasar, Arik air ta nada masu bata mai kuma tana biyan kudin inshoranta.
“Bisa ga sake dubin takardun iinshoran da akayi, Arik air zata cigaba da aikin ta misalin karfe 11na safiyar laraba,14 ga watan Satumba.
“Arik air tana nuna juyayinta ga rashin jin dadin kwastamominta kuma tayi alkawarin sake musu tiketin jirgin su.”
The post Kamfanin jirgin Arik air sun koma aiki appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.