Bishof Shepered Bushiri yayi ikirari wuta tazo daga sama
Wani bishof yayi ikirarin cewa wuta ta sauko daga lahira zuwa ga daya daga cikin mambobin cocin sa lokacin bauta. Sanannen mai wa’azi dan kasar Malawi, Shepherd Bushiri ,ya kara daukar hankalin kanun labarai kan yin ikirarin cewa wuta ta sauko daga lahira dan ta kona wani a cikin taron cocin sa. Faston da aka […]
The post Bishof Shepered Bushiri yayi ikirari wuta tazo daga sama appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
Wani bishof yayi ikirarin cewa wuta ta sauko daga lahira zuwa ga daya daga cikin mambobin cocin sa lokacin bauta.
Sanannen mai wa’azi dan kasar Malawi, Shepherd Bushiri ,ya kara daukar hankalin kanun labarai kan yin ikirarin cewa wuta ta sauko daga lahira dan ta kona wani a cikin taron cocin sa.
Faston da aka fi sani a matsayin Major1, wanda ya taba kawo rudani lokacin da ya taba cewa mala’iku sun taba sau kowa a taron shi na shekara ta 2015, yace wanda ke kokonto mu’ujizar shi ya hadu da wuta da ta fado daga lahira a jiya lokacin da suke bauta.
Mai kula da cocin ECG na Malawi ya rubuta haka a shafin sa na Facebook.
Mu’ujiza ta ranar lahadi a zahiri: kar kayi musu ko kokonto da ikon Ubangiji, kamar yadda Faston ya cigaba da yin wa’azi da bayyana karfi da girma na Ubangiji, wani abu na ban al’ajabi ya faru.
Wani mutum ya rugo da gudu yana ihu kuma yazo gurin Major1, yana neman gafara, ga mamakin kowa, wannan mutumin ya riko konanniyar riga.
Ya bayyana ma mutane yana shakkun abunda akeyi a gurin, amma amsar da muka samu ita ce wuta daga sama ta sauko ta fado mashi!!! .
Dan haka ina shawartarku kada ku taba kalu balantar ubangiji, yana ko ina, kuma ze iya taba maku zukatan ku.
Me kake/kike tunani?
The post Bishof Shepered Bushiri yayi ikirari wuta tazo daga sama appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.