Tsohon mataimakin shugaban kasa ya bayyana ainahin matsalar inyamurai
– Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alex Ekwueme yace inyamurai basu da hadin kai kamar yadda suke a baya.
– Yace yan arewa suna cewa inyamurai sune mutane masu amfani bayan ya halicci turawa.
– Ekwueme yayi kira ga inyamurai su yadda da junansu kuma su dawo da hadin kai kamar a baya.
Mataimakin shugaban kasa na Jamhuriya ta 2, Dakta Alex Ekwueme yace, ainahin matsalar inyamurai a yau shine rashin yarda.
Lokacin da yake magana a taron yan kasuwa da bikin bada kyautuka wanda kungiyar Anambra Consencus Project (ACP) suka shirya, dan girmama manyan yan kasuwa a fadin manyan kasuwannin jahar Anambra guda 57, tsohon mataimakin shugaban kasa ya tuna yadda inyamurai suke da hadin kai a baya da kuma bayan Najeriya ta samu yancin kai.
Yayi mamakin yadda abubuwa suka lalace tsawon shekaru cewa ba sauran hadin kai tsakanin jahohin inyamurai a kasar nan, Vanguard ta ruwaito.
KU KARANTA KUMA: Jibril ya tona asirin yadda yan majalisa ke kashe kudi
“Lokacin da na dawo Najeriya bayan nayi karatu kasar waje, nayi aiki da ESSO West Africa limited kuma aikin ya kaini a birane da yawa a arewacin Najeriya, sai na gano cewa ba wani wuri da zaka je kasar nan ba inyamuri, kuma suna kokari matuka.
“In kana so ka samu sayen maganin APC a ko wane wuri a arewa, Kano, Maiduguri, Kaduna , da sauran su, zaka sama inyamurai ke sai dawa, inyamurai suna da kasuwanci wanda har yasa yan arewa suna cewa bayan halittar bature, inyamurai sune halittar da ubangiji yayi mai amfani.
Dan haka tsohon mataimakin shugaban kasar yace “ya kamata inyamurai su hada kai, kuma su yarda da juna kamar yadda suke a baya.”
Kamar yadda ya bayyana wannan ita ce hanyar da zata sa su cigaba.
Ya kara bama inyamurai shawara da su kara hankali gurin habbaka kasuwanci.
The post Tsohon mataimakin shugaban kasa ya bayyana ainahin matsalar inyamurai appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.