Hukumar EFCC sun nemi da asa dokar da zasu samu wani kaso daga kudin da suke kwatowa
– EFCC sun nemi da a saka dokar da zasu iya samun wani kaso daga kudaden da suke kwatowa.
– Hukumar tace wannan abunda akeyi ne a kasashen da suka cigaba.
Ga wasu zasu iya ganin kamar tambayar ta zama bakon abu, Hukumar hana cin hanci da rashawa EFCC ta nemi da a rika bata wani kaso daga cikin kudaden da suke kwatowa.
Hukumar ta hana cin hanci da rashawa an kafa ta a lokacin mulkin Olusegun Obasanjo wadda aka dora ma alhakin hana cin hanci da satar kudin gwamnati.
Jaridar Trust ta ruwaito cewa shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu ya nemi da a saka dokar da zata ba hukumar damar aje wani dan kaso daga kudin da hukumar take kwatowa.
David Turaki mataimakin daraktan tsare-tsare da dokoki na hukumar wanda ya wakilci shugaban hukumar a taron kungiyar hana cin hanci wanda masu ba shugaban kasa shawara kan yaki da cin hanci PACAC suka shirya a Abuja.
KU KARANTA KUMA: ‘Yan sanda sun kama wasu manyan barayi su 2 wan’anda suka
Yace “bada wani dan kaso daga kudin da aka kwato abin da akeyi ne a kasashen da suka cigaba.
Yace “a tsarin dokar wasu kasashe kamar UK, yace abunda aka samu in an samu masu laifi, ana amfani da su gurin habbaka hukumar. A EFCC muna ta fadi tashi shekaru da yawa dan mu samu mu bude hedikwata., kuma in na tuna yawan biliyoyin da muka kwata, ina ganin abunda zamu yi na cigaba in an bamu damar samu wani kaso daga abunda muka kwato mu saka a hukumar mu.
Abunda ya shafi hukumar shine alhakin gurfanar da mai laifi a gaban kotu, amma a wani bangaren dole mai laifi ya tabbatar mana da abunda ya tara yayi dai dai da abunda yake yi na yau da kullum”.
The post Hukumar EFCC sun nemi da asa dokar da zasu samu wani kaso daga kudin da suke kwatowa appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.