Dan wasan Real Madrid ya bayyana kokarin kasar sa ta Germany
Kasar Germany dai ta bube gasar ta ta cin kofin kasashen turai da yin nasara a kan kasar Ukraine da ci 2-0 a kasar France.
Kungiyar Real Madrid a wani wasa
Dan wasa Shkodran Mustafi dai ne ya saka kwallon ta farko da kai cikin ragar Ukraine din wanda Pyatov yake tsarewa a cikin minti na 18 da fara wasa. Shikau Toni Kroos din wanda kuma shine aka ba gwarzon wasan yace dole ne kasar tasa su dora daga inda suka gaba wasan kuma su kara kokari.
KU KARANTA: Mummunar ambaliyar ruwa ta afka ma Abakaliki
A cewar sa ” wannan ai somin tabi ne. Samun nasar da 2-0 ba tare da an saka mana kwallo ba tabbas nasara ce babba a gare mu. Mun yi kokari sosai sannan kuma mun taka ledar yadda ya kamata”.
Sannan ya cigaba da cewa: “a cikin mintuna 15 na karshen zangon farko na wasan bamu yi kokari ba sosai don kuma koda ma an saka mana kwallo ba zamu yi korafi ba. Amma daga bisani sai muka mamaye wasan sannan kuma muka cigaba da yin kokari har aka tashi.
Kroos din kuma ya yaba ma dan bayan kungiyar Valencia din sakamakon kokarin sa duk kuwa da kasance war Mats Hummels da Antonio Rudiger ba su nan.
The post Dan wasan Real Madrid ya bayyana kokarin kasar sa ta Germany appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers.