sama da ma’aikatan NNPC 1500 basu bayyana kadarorinsu
– Sama da ma’aikatan NNPC guda 1500 , hasali masu manyan kujeru ne basu bayyana kadarorin su ba har yanzu – Wannan saba dokar ofishin kula da halin ma’aikata ne karara Dama NNPC sananiya ce da rashawa da al mundahanan sama da shekaru 20 yanzu, Jaridar New Telegraph ta binciko cewa sama da ma’aikatan ta 1500 […]
The post sama da ma’aikatan NNPC 1500 basu bayyana kadarorinsu appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers.
– Sama da ma’aikatan NNPC guda 1500 , hasali masu manyan kujeru ne basu bayyana kadarorin su ba har yanzu
– Wannan saba dokar ofishin kula da halin ma’aikata ne karara
![NNPC](https://i.onthe.io/vllkytgm2vurgmftc.88b40195.jpg)
NNPC
Dama NNPC sananiya ce da rashawa da al mundahanan sama da shekaru 20 yanzu, Jaridar New Telegraph ta binciko cewa sama da ma’aikatan ta 1500 ne suka yi kunnen kashi da umurnin bayyanar da kadarorin su
A watan mayu 2016, kashi 70 cikin 100 na ma’aikata 5000 ne suka bayyanar da kadarorin su. Kasha 70 din ma ,an gano su ne ta wani yunkurin da aka fara ranar talata 4 ga watan agusta 2015 domin karfafa sarrafe sarrafen kamfanin, da haskaka dabaru domin daukaka cin riba.
“Abin da ke faruwa kafin zuwan wannan sabon directa manajan Dr. Ibe Kachiku shine,ba wanda ya damu ko sun bayyana kadarorinsu ko basu bayyana ba”. Wani babban ma’aikaci ya fada
“A labarin ayyukan kudi da NNPC ke fiddawa a kowani wata a shafin ta na yanar gizo, saboda tabbatar da cewa a tare kowani hanya na rashewa da almundana, a watan mayu, kamfaninin ta bayyana cewa kasha 70 ne suka bayyana kadarorinsu.”
Ma’aikatan NNPC a baje suke, wadansu na hedkwata a Abuja, sauran na ofishin sashin su a Legas,kaduna ,fatakwal,da wari. NNPC na da ofishin kasar waje ma a birnin landan,kasar Ingila. A wani rahoton KPGM a disamba 2011, wanda ma’aikatar kula da sha’anin kudi ta rantsar domin tabbatar da cewan ba’a saba doka, hana satan kudi, da tare biliyoyin nairori shiga asusun gwamnati.
Masu binciken kudin sun samu cewan a tsakanin shekaran 2007 da 2009 kadai, kamfanin NNPC ta zare kudi naira biliyan 28.5 da sunan kudin tallafin man fetur. Har wa yau ,bata amsa tambayar yadda akayi da kudin ba.
The post sama da ma’aikatan NNPC 1500 basu bayyana kadarorinsu appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers.