Bamu samu kyautan matar Buhari ba – Iyayen matan Chibok
-Iyayen yan’ matan Chibok sun bayyana cewa har yanzu basu samu karban kyautan naira miliyan N30 da Aisha Buhari tayi masu ba. -Kwanan nan matar shugaban kasa, ta gabatar da takadar da ke nuni da kyautan naira miliyan N55 ga iyayen, yan matan makarantar Chibok. Wasu iyayen yan’matan Chibok, sun bayyana cewa, har yanzu basu […]
The post Bamu samu kyautan matar Buhari ba – Iyayen matan Chibok appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers.
-Iyayen yan’ matan Chibok sun bayyana cewa har yanzu basu samu karban kyautan naira miliyan N30 da Aisha Buhari tayi masu ba.
-Kwanan nan matar shugaban kasa, ta gabatar da takadar da ke nuni da kyautan naira miliyan N55 ga iyayen, yan matan makarantar Chibok.
Wasu iyayen yan’matan Chibok, sun bayyana cewa, har yanzu basu sami karban kyautan naira miliyan N30 da matar shugaban kasa, Aisha Buhari ta yi ba.
Kwanan nan matar shugaban kasa, ta gabatar da takarda da ke nuni da kyautan kudi, naira miliyan N55, ga iyayen yan’matan Chibok tare da mazan makarantar Buni Yadi da suka bata.
Iyayen yan’matan da suka bata, suna zargin wasu mutane na samun kudi da sunan su.
A cewar wani rahoto daga jaridar Punch, Yana Galla, sugaba a kungiyar iyayen yan’matan makarantar Chibok da suka bata, wadanda suke zaune a cikin garin Chibok da kauyukan kewaye, sun kore jita-jitan cewa an raba kudaden a tsakanin su.
Galla ta ce har yanzu kudin na tare da mataimakiyar matar shugaban kasa.
Ta ce, bayan taimakon N100,000 da suka samu daga gwamnan jihar Borno, a watan Augusta na shekara ta 2015, taimako na karshe da suka samu tun sannan, shine N5,000, wanda suka samu daga kamfanin MTN Foundation, a ranar tunawa da sace yan’matan, a wannan shekaran.
Ta ce: “Mun dai kawai ji cewa an ba da wani abu, kuma mun kasance muna jira ya iso gare mu. zai iso yau ko sai gobe? haka ne yake kasancewa a ko da yaushe, alhalin kuwa taimakon baya taba samun mu.”
A cikin kyautan naira miliyan N30 da Aisha Buhari tayi, Ladi ta ce: “Abunda muka taba samu shine zunuwa biyu tare da N5,000.
“Idan har an saki kudin, toh bai iso mu ba. Naira 5,000 din da nace an bamu tare da zannuwa, an bamu ne lokacin da aka yi addu’an shekara biyu da batan ya’yan mu.”
Wata daga cikin iyayen da aka rahoto, Ayama Pogu, ta bukaci gwamnati da tayi tunani akan wadanda suke ikirarin wakiltan su.
A halin da ake ciki, Sojojin Najeriya sun bayyana cewa, suna kewaye da yan Boko Haram a dajin Sambisa. sun ba da rahoto cewa yan ta’adan bazasu iya kai hari a sauran al’umma ba.
The post Bamu samu kyautan matar Buhari ba – Iyayen matan Chibok appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers.